IQNA

23:51 - July 26, 2019
Lambar Labari: 3483882
Bangaren kasa da kasa, kungiyar Hamas ta yi na’a da kalaman shugaban falastinawa Mahmud Abbas dangane da dakatar da duk wata alaka da Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga jaridar Quds Al-arabi cewa, Hamas ta fitar da wani bayani wada a cikinsa ta nuna goyon bayanta ga kalaman da Mamud Abbas Abu mazin ya yi kan alakar gwamnatin falastinawa da Isra’ila.

Bayanin ya ce Hamas tana goyon bayan matakin dakatar da uk wata hulda tsakanin gwamnatin falastinawa da kuma Isra’ila, sakamakon yadda Isra’ila take cin Karenta babu babbaka da yin fatali da dokokin kasa da kasa.

A jiya ne shugaban Falastinawa Mahmud Abbas ya sanar da cewa, gwamnatin falastinawa ta dakatar da duk wata alaka da ke tsakaninta da Isra’ila, sakamkon ci gaba da rusa gidajen falastinawa da Isra’ila ke yi a gabashin birnin Quds.

Abbas ya ce wannan abin da Ira’ila take yi ya kawo karshen duk wata tuntubar juna tsakaninta da su, kuma dukkanin bangarorin falastinawa za su hada kai domin kalu balantar wannan mataki.

Baya ga Hamas kungiyoyin falastinawa da dama sun nuna gamsuwarsu da matakin na Mahmd Abbas, tare da shan alwashin mara masa baya kan hakan.

Hamas ta ce tana fatan ganin abin da Abbas ya fada a aikace, domin kada ya yaudaru da wasu alkawulla ko wata barazana da za ta sanya shi ya sauya matsayinsa.

 

3829977

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Hamas ، Palestine
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: