IQNA

Kotu Ta Dage Sauraren Shari'ar Sheikh Zakzaky

20:27 - July 29, 2019
Lambar Labari: 3483892
Bangaren kasa da kasa, kotun Kaduna da ke sauarren shari’ar Sheikh Ibrahim Zakzaky ta dage sauraren shari’ar har zuwa ranar 5 ga watan Agusta mai kamawa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, alkalin da ke sauraren shari’ar Dariuos Khobo yadage zaman sauarren shari’ar ne bisa hujjar cewa zai duba dukkanin hujjoji da bangarorin biyu suka gabatar, na lauyoyin gwamnati, da kuma lauyoyin sheikh Zakzaky, inda a mako mai zuwa zai yanke hukunci na karshe.

Babban lauya da ke jagorantar lauyoyin da suke kare Sheikh Zakzaky Femi Falana San, ya sheda wa kotun cewa, wanda yake karewa yana fama da matsananciyar rashin lafiya, kuma suna bukatar kotu ta bayar da damar fitar da shi domin kula da lafiyarsa.

A nasa bangaren lauyan gwamnati ya kalubalanci lauyoyin sheikh Zakzaky kan batun rashin lafiyar tasa, inda ya ce za a iya duba lafiyarsa a cikin Najeriya, ba sai an fitar da shi zuwa kasashen ketare ba.

Ana tsare ad Sheikh Zakzaky ne dai tun a karshen shekara ta dubu biyu da sha biyar, bayan farmakin da sojoji suka kai gidansa, tare da kashe daruruwan mabiyansa, bisa hujjar da suka bayar na cewa mabiyansa sun tare wa babban hafsan sojin kasa hanya, da kuma yunkurin halaka shi, zargin da Harkar musulunci karkashin jagorancin Sheikh Zakzaky ta musunta.

3830894

 

captcha