IQNA

23:53 - August 06, 2019
Lambar Labari: 3483918
Bangaren kasa da kasa, an fara aiwatar da shirin horar da dubban daliban kur’ani mai tsarki a kasar Qatar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin iloveqatar cewa, a jiya an fara aiwatar da shirin horar da  daliban kur’ani dubu 5 da 969 a cibiyoyi  139 a kasar Qatar.

Bayanin ya sce shirin yana gudana karkashin kulawar kwamitoci 466 da aka kafa, kwamitoci 17 ke gudanar da ayyukansu da safe, yayin da 449 kuma suke gudanar da shirinsu da yamma

M’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ce dai take dayukar nauyin wannan shiri har sau uku a kowace shekara, tare da halartar dubban dalibai.

 

3832995

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: