IQNA

An Kashe Dan Uwan Jagoran Ansarallah

23:52 - August 09, 2019
Lambar Labari: 3483929
An Kashe Dan Uwan Jagoran Ansarallah
Bnagare kasa da kasa, tashar Almasirah ta kasar Yemen ta sanar cewa an kashe Ibrahim Badruddin Alhuthi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga Almasirah cewa, a yau Juma’a wasu ma’aikatan kawancen Amurka da Isra’ila da saudiyya da ke kaddamar da hare-hare kan al’ummar Yemen, sun kashe Ibrahim Baduddin Alhuthi.

Ma’ikatar harkokin cikin gida ta kasar Yemen ta sana da cewa, an shiga bincike domin gano masu hannu a cikin lamarin.

Haka nan kuma tashar ta mika sakon ta’aziyya  ga Sayyid Abdulmalik Badruddin Alhuthi jagoran kungiyarn Ansarallh.

3833648

 

 

 

captcha