IQNA

22:58 - August 10, 2019
Lambar Labari: 3483934
Bangaren kasa da kasa, Falastinawa 4 ne suka yi shahada a yau bayan da sojojin Isra’ila suka yi ruwan wuta a kansu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Reuters cewa, a  yau sojojin Isra’ila sun yi ruwan wuta kan falastinawa a kusa da shingen da yahudawa suka saka a kan iyakan Gaza, inda suka kashe falastinawa hudu.

Sojojin Isra’ila sun kare kansu da cewa wadanann falastinawan suna shirin kai wasu hare-hare ne a kansu, ta hanyar harhada wasu abubuwa da ake zaton bam ne.

Sai dai bayan kashe wadannan fal;astinawa ba a samu komai tare da su ba, illa dai kawai suna tafiya ne a kan hanyar da ke kusa da wurin a lokacin sojojin yahudawan suak kashe su.

3833771

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: