IQNA

23:50 - August 14, 2019
1
Lambar Labari: 3483947
Bangaren kasa da kasa, sheikh Ibrahim Zakzaky ya fitar da bayani kan yanayin da ake ciki a asibitin da yake a kasar Indiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Masud Shajare ya sanar da cewa  Sheikh Zakzaky ya fitar da wani bayani na sauti daga asibitin da yake a kasar Indiya.

Shugaban harkar musulunci a Najeriya Sheikh Ibrahim Yakubu El-Zakzaky ya bayyana rashin gamsuwarsa da yanayin da ya sami kansa a kasar Indiya.

Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda ya aika da sakon na murya, ya ce; An sa shi a karkashin tsaro mai tsanani ta yadda hatta a cikindakin asibitin da yake ciki da akwai jami’an tsaro masu dauke da makamai.

Har ila yau, Sheikh Zakzaky ya nuna rashin amintarsa da likitocin da za su yi masa aiki, don haka yake cewa:

“Insha Allahu dai gaskiyar magana ita ce akwai bukatar mu koma gida tundadai an yarda mu je wani wuri a waje domin magani tunda India lallai ba ta zama wurin aminci ba yanzu. Sai dai mu koma gida, daman akwai wadansu kasashe da suka yi tayi na cewa za su karbe mu in mun je.

 

3834978

 

Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Allah yakara daukaka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: