IQNA

Nasrullah Ya Aike Da Sako Jinjina Ga Zarif

22:55 - August 15, 2019
Lambar Labari: 3483950
Nasrullah Ya Aike Da Sako Jinjina Ga Zarif
Bangaren kasa da kasa, Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta Lebanon ya jinjinawa ministan harkokin wajen Iran akan tayin dakansa wajen kalubalantar Amurka

Kamfanin dillancin labaran iqna, a wata wasika da babban kwamandan na kungiyar Hizbullah ya aikewa da ministan harkokin wajen na jamhuriyar musulunci ta Iran, Sayyid Hassan Nasarallah ya ce;

Na rubuto muku wasika ne saboda in bayyana goyo baya da girmamawa a gare ku,saboda shigar da ku cikin jerin sunayen daukaka.

Sayyid Nasarallah yana ishara ne da jerin sunayen mutanen da Amurka take kakabawa takunkumi da a bayan nan ta shigar da sunan ministan harkokin wajen na Iran.

A cikin wasikar, babban sakataren kungiyar ta Hizabullah ya bijiro da yadda yakin kwanaki 33 na 2016 ya kasance ta fuskar diplomaisyya, da yadda sakataren harkokin wajen Amurka ya bukaci a tsagaita wutar yaki.

3835046

 

captcha