IQNA

23:01 - August 15, 2019
Lambar Labari: 3483952
Bangaren kasa da kasa, kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya zai gudanar da zama kan halin da ake ciki a yankin Kashmir na kasar India.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, gwamnatin kasar China ta bukaci da a gudanar da zaman gaggawa kan batun Kashmir, bayan da firayi ministan kasar Pakistan Imran Khan ya bukaci hakan.

Zaman wanda zai gudana a yau ba tare da halartar ‘yan jarida da sauran jama’a da mambobin kwamitin ba, zai yi dubi kan halin da ake ciki a yankin na Kashmir, da kuma lalubo hanyoyin warware rikicin da yankin ya fada a cikin, bayan da Indiya ta soke kwarkwaryan cin gishin kai da yankin yake da shi.

Tun kwanaki goma da suka gabata ne gwamnatin kasar Indiya ta sanar da soke cin gishin kan da yankin Kashmir yake da shi, lamarin da ya jefa yankin a cikin wani mummunan yanayi da rashin tabbas.

Bisa doka mai lamba 370 da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar India, yankin Kashmir na da cin gishin kaia  cikin dukkanin harkokinsa, inda banda batutuwan tsaro da kuma siyasar harkokin waje.

Wannan lamari dai ya jawo tayar da jijiyoyin wuya tsakanin India ta Pakistan, inda a halin yanzu suka yanke alakokin da ke tsakaninsu na diflomasiyya, da kuma yi wa juna kallon hadarin kaji.

 

3835160

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، hadarin kaji ، India ، Pakistan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: