IQNA

23:51 - August 19, 2019
Lambar Labari: 3483964
Bangaren kasa da kasa, ministan harakokin wajen Jodan ya kirayi jakadan Isra'ila domin nuna masa rashin amincewar kasarsa kan hare-haren wuce gona da iri kan masallacin Qudus.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kakakin ma'aikatar harakokin wajen Jodan Sufyan Salman Al-Kudat na cewa kasarsa ta kira jakadan Isra'ila tare da mika masa wasikar nuna rashin amincewa da hare-haren baya-bayan da dakarun Isra'ila suka kai kan masallacin Qudus, sannan sun bukaci Isra'ila da ta kawo karshen harin wuce gona da irin da take kaiwa kan masallacin.

Al-Kudat ya kara cewa kasarsa ta yi tir da rufe kofofin masallacin na Qudus da kuma yadda dakarun haramtacciyar kasar Isra'ila ke hana Falastinawa shiga masallacin, tare da neman Isra'ila ta yi aiki da alkawarin da ta dauka na bin dokokin kasa da kasa.

Wannan mataki da kasar Jodan ta dauka na zuwa ne , bayan furicin da ministan tsaron cikin gidan Isra'ila ya yi na cewa lokaci ya yi da za a canza yanayin masallacin Qudus ta yadda Yahudawa za su samu damar shiga ciki, su kuma gudanar da ibadunsu .

 

3835941

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Jordan ، jakada
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: