IQNA

23:56 - August 19, 2019
Lambar Labari: 3483966
Bangaren kasa da kasa, Daesh ta dauki alhakin kai harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da sattin a birnin Kabul na kasar Afghanistan.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kungiyar ‘yan ta’adda ta Daesh ta sanar da cewa, ita ce ta shirya da kuma kaddamar da harin ta’addanci a kan wani taron bikin aure a birnin Kabul fadar mulkin kasar Afghanistan, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 63, da kuma jikkatar wasu 180 na daban.

Jami’an tsaron kasar Afghanistan dai sun ce an kai harin ne da misalin karfe goma da rabi na dare a ranar Asabar, a lokacin da mutane suke halartar wani taron bikin aure a wani babban dakin taruka da ke birnin, inda inda mutane da dama suka rasa rayukansu wasu kuma suka jikkata.

Wadanda suka sheda abin da ya faru sun bayyana cewa, wani dan kunar baki wake ne ya tarwatsa kansa da wata jigidar bama-bamai a tsakiyar jama’a a cikin dakin taron.

Bayan faruwar lamarin dai kungiyar Taliban ta sanar da cewa ba ta da hannu a wanann hari, kafin daga bisani kungiyar daesh ta sanar da cewa ita ce ke da alhakin harin.

 

3835900

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Daesh ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: