IQNA

23:57 - August 20, 2019
Lambar Labari: 3483970
Bangaren kasa da kasa, Umar Albashir tsohon shugaban Sudan ya gurfana  a gaban kotu a cikin tsauraran matakan saro.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a jiya kotun da ke sauraren shari’ar tsohon shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ta gudanar da zamanta a birnin Khartum fadar mulkin kasar Sudan.

Zaman kotun dai ya gudana ne tare da halartar Albashir da kuma lauyoyinsa gami da masu shigar da kara da kuma halartar dukaknin alkalan kotun.

Kafin wannan lokacin dai an sanar da cewa kotun za ta gudanar da zamanta ne a bayyane, amma a lokacin gudanar da zaman an hana mutane shiga, kamar yadda haka hana ‘yan jarida shiga da kayan daukar rahotanni.

A yayin da yake amsa tambayoyi kan kan tuhumar da ake yi masa ta mallakar kudaden haram, Albashir ya bayyana cewa dukkanin kudaden da aka samu tare da shi bayan hambarar da gwamnatinsa, ya same su ne daga yariman Saudiyya.

 Albashir ya ce yariman ya ba shi dala miliyan casain  lakadan, ba ta hanyar banki ba a shekara ta dubu biyu da sha biyar domin Sudan ta aike da sojojinta zuwa Yemen domin su yi wa Saudiyya yaki a kasar, kuma Albashir ya amince da hakan bayan karbar wadannan makudan kudade, wadanda ba a saka su cikin lissafin baitul mali na gwamnati ba.

Dangane da wasu makudan miliyoyin daloli da aka samuacikin gidan Albashir a lokacin da aka hambarar da gwamnatinsa, ya bayyana cewa ya karbi wadannan kudaden ne daga bisani a matsayin kyauta daga yariman Saudiyya Muhammad Bin Salman ta hanyar shugaban ofishinsa, kuma wadannan kudade ba su da wata alaka da gwamnatin Sudan.

 

 

 

3836163

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: