IQNA

23:57 - August 23, 2019
Lambar Labari: 3483979
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Faransa ya byyana cewa basu da wata fata dangane da shirin Amurka na yarjejeniyar karni.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Palestine cewa,a  zantawarsa da jaridar Kan ta Isra’ila, shugaban kasar Fransa Emmanuel Macron ya byyana cewa daga bangarensu babu wata fata dangane da shirin shugaban Amurka Donald Trump na yarjejeniyar karni da ya gabatar.

Macron ya ce batun Palastinu da Isra’ila ba batu ne wanda yake daga cikin abubuwan da za a tattauna a taron G7 ba.

Ya ci gaba da cewa, warware matsalar Falastinawa abu ne da ke bukatar cimma matsaya da amincewar dukkanin bangarorin rikicin biyu, ba abu ne da za a dora shi a kan daya bangaren ba.

A yau ne za a fara taron G7 a Faransa tare da halartar mambobin kungiyar.

An fara wannan taro ne tun 1975 tare da halartar Jamus, Faransa, Italiya, Birtaniya, Japan da kuma Amurka, daga bisani kuma Canada ta shiga cikinsu.

 

3836758

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: