IQNA

Amurka Ta Yarda Cewa Isra'ila Ce Ta Kai Hari A Iraki

23:02 - August 24, 2019
Lambar Labari: 3483982
Bangaren kasa da kasa, jami'an gwamnatin Amurka sun tabbatar da cewa Isra'ila ce ta kaddamar da hare-harea kan wuraren ajiyar makamai na Hashd shabi a Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna, jami'an Gwamnatin kasar Amurka sun ta tabbatar da cewa jiragen yakin Haramtacciyar kasar Isra’ila ne suka kai hare-hare kan rumbon ajiyar makamai na dakarun Hashdusha’bi na kasar Iraqi a cikin kwanakin da suka gabata.

Tashar talabijin ta Aljazeera ta nakalto jami’an gwamnatin Amurka suna tabbatar da labarin a yau, sannan sun bayyana cewa jiragen yakin wadanda ake sarrafasu daga nesako wato “Drons” ne suka kai hare-haren don lalata rumbun makamai na dakarun hashdushaabi, wadanda suka ce wani bangaren ne na makaman kasar Iran.

Kafin wannan tabbacin dai, majiyar dakarun hashdushaabi ta zargi Isra'ila da kai wadannan hare-hare, sannan ta tabbatar da cewa sun yi haka ne tare da taimakon sojojin kasar Amurka da suke cikin kasar ta Iraqi.

Dakarun hashdushaabi dai sune mayakan sa kai wadanda suka kori mayakan kungiyar da’ish daga arewacin kasar ta Iraqi tare da taimakon takwarorinsu na kasar Iran.

Kungiyar Daesh wacce kasar Amurka ta samar,ta mamaye mafiyawankasar Iraqi a shekara ta dubu biyu da sha hudu, amma tare da taimakon mayakan sa kai na rundunar Hashdushaabi sun kori mayakan na daesh daga kasar ta Iraqi, amma tuni Amurka ta sanya kungiyar cikin jerin kungiyoyin yan ta’adda a wajenta, saboda tallafi da Amurka ta ce tana samu daga kasar Iran domin gudanar da ayyukanta.

3836855

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha