IQNA

23:03 - August 24, 2019
Lambar Labari: 3483983

Albashir ya Sake Gurfana A Gaban Kuliya A Karo Na Biyu

Bangaren kasa da kasa, hambararren shugaban kasar Sudan Umar Hassan Albashir ya sake gurfana agaban kuliya domin fuskantar shari'a.

Albashir ya Sake Gurfana A Gaban Kuliya A Karo Na Biyu

Kamfanin dillancin labaran iqna, An kammala sauraron shir’ar da akewa tsohon shugaban kasar Sudan Umar Hassan Al-Bashir a karo na biyu a yau Asabar a wata kotu a birnin Khartun babban birnin kasar, sannan an sanya ranar 31 ga watan da muke ciki a matsayin ranar da za’a saurari shari’ar a karo na ukku

Tsohon shugaban na Sudan ya sami halartar zaman shari’ar a karo na biyu a yau Asabar da kansa, sannan shugaban tawagar lauyoyi 130 masu kare shi mai suna Ahmad Ibrahim Tahir ya bayyana cewa sun gabatarwa kotun bukatar a bada belin tsohon shugaban kasar a zamanta na yau.

A ranar litinin da ta gabata ce aka gurfanar da tsohon shugaban kasar a gaban kotu a karon farko, kuma tawagar masu gabatar da kara wacce ta kunshi lauyayoyin gwamnati 7 ne suka karantawa tsohon shugaban kasar tuhume-tuhumen da ake masa, wadanda suka hada da kashe masu zanga-zanga da kuma ajiye kudade kasashen waje a gidansa.

Sai kuma a zaman sauraron shari’ar a yau Asabar lauyoyi masu gabatar da kara sun gabatar da shaidu guds 3 wadanda suka binciki gidan tsohon shugaban kasan bayan an yi masa juyin mulki, akwai sauran masu bada shaida wadanda za’a gabatar a zaman sauraro shari’ar nan gaba.

Har’ila yau wasu daga cikin dangin tsohon shugaban kasar sun sami halartar zaman shari’arsa ta yau Asabar, sannan wasu mago bayansa kuma sun yi gangami a gaban kotun inda suke yin allawadai da shari’ar da ake masa.

3837083

 

captcha