IQNA

23:57 - September 01, 2019
Lambar Labari: 3484008
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar babban taron baje kolin abincin Halalabirnin Nairobi fadar mulkin kasar Kenya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa ne za a bude babban baje kolin abincin Halal karo na hudu a birnin Nairobi na Kasar Kenya.

Rahoton ya ce wannan taron baje kolin abincin halal zai samu halartar kamfanoni daga kasashen duniya daban-daban, da kuma fitattun mutane kimanin 300 da aka gayyata daga kasashe duniya.

Wannan taro dai ana gudanar da shi ne karkashin kulawar ma’aikatar kula da harkokin tattalin arziki da saka hannayen jari ta kasar Kenya, wadda take daukar nauyin shiriyawa da kuma gudanar da wannan taro na kasa da kasa, wanad kuma wannan shi ne karo na hudu da zaa gudanar da shi.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ne dai ya cimma matsaya tare da wasu kamfanonin kasashen musulmi masu samar da abincin halal tun a wa’adin mulkinsa na farko, inda kuma yake gayyatar sauran kamfanonin kasashen Afrika da su saka hannayen jari akamfanonin abincin Halal da suke gudanar da ayyukansu a kasar Kenya.

3838798

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Kenya ، Nairobi ، abincin halal
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: