IQNA

23:27 - September 04, 2019
Lambar Labari: 3484016
Bangaen kasa da kasa, dakaun Yemen tare da dakarun sa kai na Ansarullah sun kai hari kan filin jiragen sama na Najran.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a wani bayanai da Kakin dakarun sojin kasar Yamen Brigedier Janar Yahya Sare ya fitar a ranar Talata ya nuna cewa dakarun sojin kasar sun harba makamai masu linzami kirar badr one a filin tashi da saukar jiragen sama na Najran dake kasar saudiya, kuma ya jawo cikasa sosai a zirga zirgar jiragen sama.

Ya ci gaba da cewa harin yazo ne a matsayin mai da martani game da hare haren wuce gona da iri da dakarun hadin guiwa da kasar saudiya ke jagoranta ke kai wa kan kasar Yamen, kuma sun yi kokari wajen ganin hare haren basu  shafi fararen hula ba,

Kasar saudiya da kawayenta sun shelatan yaki kan kasar Yamen ne a shekara ta dubu da sha biyar da zimmar dawo d shugaba kasar kan karagar mulki.

Kididdigar da majalisar dinkin duniya ta fitarya nuna cewa ya zuwa yanzu sama da mutane sama da dubu casain suka mutu ko suka samu raunuka sakamkon hare haren na Saudiyya da take kaiwa kan fararen hula a cikin shekaru hudu da rabi.

Haka nan kuma sama da mutane miliyan ashirin da hudu ke neman gajin gaggawa yayin da sama da miliyan goma ke fama da matsananciyar yunwa.

3839723

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Ansarullah ، yemen ، Saudiyya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: