IQNA

23:55 - September 10, 2019
Lambar Labari: 3484037
Bangaren kasa da kasa, akalla mutane 31 sun rasa rayukansu wasu da dama kuma sun jikkata sakamakon tirmutsitsi a taron Ashura a Karbala.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Saif badr kakakin ma’aikatar kiwon lafiya a lardin Karbala ya fadi yau cewa, mutane 31 ne suka rasa rayukansu, wasu kimanin 100 kuma suka jikakta a tirmutsitsin miliyoyin mutane da aka samu a yau a taron Ashura a Karbala.

Ya ce 10 daga cikin wadanda suka samu raunuka suna cikin mawuyacin hali, amma ana kula da su a asibitocin birnin.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa an samu tirmutsitsin ne a kofar Raja ta hubbaren Imam Hussain (AS) sakamakon yawan jama’a.

3841374

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: