IQNA

23:37 - September 15, 2019
Lambar Labari: 3484053
Bangaren kasa da kasa, kakakin rundunar sojin Yemen ya sanar da mayar da martani kan hare-haren Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, sakamakon hare-haren ramuwar gayya da dakarun kasar Yemen suka kaddamar kan babban kamfanin mai da iskar gas na kasar Saudiyya, yawan danyen man da kasar take fitarwa a kowace rana ya ragu da kusan kashi hamsin cikin dari.

Ministan main a kasar Saudiyya ya sanar da cewa, hare-haren sun jawo tashin gobara a manyan ma’aikatu biyu na kamfanin, wanda hakan ya yi sanadiyyar konewar tataccen man fetur da ya kai ganga miliyan biyar, kamar yadda hakan ya yi sanadiyyar tarwatsewar wasu manyan tankunan adana iskar gas.

Shugaban Amurka ya tuntuni yariman Saudiyya mai jiran gado jim kadan bayan kai harin, tare da tabbatar masa da cewa Amurka tana tare da Saudiyya, kuma a shirye take ta ci gaba da bata kariya da tsaro.

Kakakin rundunar sojin kasar Yemen Brigadier General Yahaya Sari ya fadi jiya a birnin San’a fadar mulkin kasar Yemen cewa, sun aike da jiragen yaki marassa matuka guda goma, wadanda kuma su ne suka kaddamar da wadannan hare-hare a kan kamfanin man an Saudiyya.

Janar Yahya ya ce, an kwashe kusan shekaru biyar a jere Saudiyya tana kaddamar da hare-hare ta sama da kasa da kuma ta ruwa a kan al’ummar kasar Yemen, tare da kashe dubban fararen hula da suka hada da mata da kananan yara.

Haka nan kuma Saudiyya ta rusa daruruwan masallatai, makarantu, kasuwanni, cibiyoyin kiwon lafiya, tashoshin wutar lantarki da na ruwan sha, tare da rusa dubban gidajen jama’a, ya ce babu wani abu mai amfani a kasar Yemen wanda ya rage ahalin yanzu wanda Saudiyya ba ta rusa shi ba, kuma tana ci gaba da yin hakan a kan idanun duniya ba tare da wata kasa tace uffan ba.

Ya ce a haka, wanann shi ne zabin da ya rage ga al’ummar Yemen, matukar dai Saudiyya ba ta dakatar da kaiwa al’ummar kasar Yemen hari ba, to kuwa kowane harin nata yana biye da martani daga kasar Yemen.

 

3842021

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Yemen ، aramco ، saudiyya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: