IQNA

23:40 - September 16, 2019
Lambar Labari: 3484056
Bangaren kasa da kasa, za a girmama mahardata kur’ani mai tsarki a makarantar Tanzil da ke kasar Australia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin makonni biyu masu zuwa ne za a gudanar da taron girmama mahardata da makaranta kur’ani mai tsarki wanda makarantar Tanzil ta shirya da ke garin Port na kasar Australia a jihar yammacin kasar.

A yayin wannan taro dai za a gayyaci fitattun mahardata da makaranta daga sassa daban-daban na kasar da ma kasashen ketare.

Haka nan kuma za a bayar da kyatuka na musamman ga masu hidima ga kur’ani mai tsarki, kama daga malamai, da mahardata da kuma makaranta.

Wannan dais hi ne karo na farko da za a fara gudanar da irin wannan taro wanda makarantar za ta dauki nauyinsa, wanda kuma ake sa ran zai ci gaba da gudana a kowace shekara.

3842469

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، shekara ، gudana ، Australia
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: