IQNA

23:01 - September 21, 2019
Lambar Labari: 3484072
Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron Iraki sun kame mutumin da ke da hannu a harin Karbala.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Saumariy ya bayar da rahoton cewa, majiyar jami’an tsaro a kasar Iraqi ta bada sanarwan cewa an kama mutumin da ya kai harin ta’addanci a kusa da mashiga ta hamsin da hudu a cikin birnin Karbala wanda yayi sanadiyar shahadar mutane sha biyu a jiya jumma;a.
Rahoton ya kara da cewa an kama mutumin ne a wani dakin cin abinci mai tazarar kilomita guda kacal daga inda ya data boma-boman.
Labarin ya kara da cewa mutumin ya dana boma-boman ne a cikin wata muta a mashiga ta hamsin da hudu zuwa cikin birnin na Karbala.
Har’ila yau labarin ya kara da cewa mutumin ya shiga motar day a danawa boma-boman ne said a ya kai wani wuri sai ya sauka barsu a karkashin kujerar da ya zauna a cikin motar, sannan ya tada su daga nesa a lokacinda motar da je kusa da inda ake gudanar da bincike a mashiga ta hamsin da hudu.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dau al-hakin kai hare-haren na jiya.

3843454

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iraki ، Karbala ، tashin bam ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: