IQNA

23:57 - October 01, 2019
Lambar Labari: 3484108
Bangaren kasa da kasa, hukumar bautar kasa NYSC a Najeriya ta amince ga mata masu bautar kasa da su saka lullubi idan suna bukata.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin jaridar Punch NG cewa, hukumar bautar kasa NYSC a Najeriya ta amince ga mata masu bautar kasa da su saka lullubi idan suna bukatar yin hakan.

Bisa wannan mata masu bautar kasa za su iya yin amfani da farin kyalle dogo ko gajere domin lullube kansu a  lokacin bautar kasa ba tare da wata matsala ba.

Bisa ga tsarin Najeriya tun daga shekara ta 1973, daliban jami’a da suka kammala karatun digiri na farko suna tafiya bautar kasa na tsawon shekara guda, wanda hakan yake da babban tasiri a cikin harkar karatu a kasar.

 

3846446

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: