IQNA

23:00 - October 05, 2019
Lambar Labari: 3484121
Bangaren kasa da kasa, an bude wata makaranta a kasar Masar da sunan fitacen dan takwallon duniya Muhammad Salah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga tashar Arab News cewa, a yau bude wata wata makarantar sakandare a lardin Bisyun a kauyen Najrij da ke tazarar kilo mita 100 daga birnin Alkhira da sunan Muhammad Salah.

Wannan makarantar an sake gina ta ne bayan rusa tsohon gininta, kuma Muhammad Salah dan asalin wanann kauye ne kuma a nan aka haife shi, kuma a wannan makarantar ya yi karatu.

An kashe kudi hard alar Amurka dubu 770 wajen sake gina makarantar, kuma Muhammad Salah ne ya bayar da kudin, kuma makarantar a halin yanzu za ta dauki wurin koyar da dalibai 2715.

Muhammad Hassan daya ne daga cikin malaman makarantar ya sheda cewa, Muhammad salah daya ne daga cikin dalibansa wadanda ya koyars da su, a halin yanzu ya zama zakaran kwallon kafa a duniya.

An saka ma wannan makaranta sunan uhammad salah ne a lokacin da ya saka wa kungiyar kwallon kafa ta Masar kwallo, wadda ta ba kasar damar zuwa gasar cikin kofin kwallon kafa na 2018.

3847274

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Muhamamd salah ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: