IQNA

22:47 - October 10, 2019
Lambar Labari: 3484139
Bangaren kasa da kasa, ofishin firayi ministan kasar Iraki ya sanar da makoki na tsawon kwanaki domin addu’a ga wadanda suka rasa rayukansu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a wani jawabi da ya yi ta gidan talbijin din kasar, pira ministan Iraqi Adel Abdul Mahdi ya bayyana cewa ya bukaci majalisa ta kada kuri’ar canzawa wasu ministoci ma’aikatunsu, kuma ya lashi takobin mika daruruwan sunayen wadanda ake zargi da hannu wajen rura wutar Zanga-zangar da ta gudana a kasar gaban kuliya manta sabo domin hukumtasu.

Har ila yau ya sanar da kwanaki 3 domin yin zaman makoki a fadin kasar, domin nuna alhini da kisan mutane dari da goma da aka da kuma jikkata sama da mutum dari shida sakamakon taho mu gama da aka yi tsakanin jami’an tsaro da masu Zanga- zangar nuna kin amincewa da kunci rayuwa da matsatsin tattalin arziki da alummar kasar ke ciki, a birnin Bagadaza da wasu yankunan dake kudancin kasar.

Ya ci gaba da cewa: mun umarci jam’ain tsaro da kada su yi amfani da harsashi mai rai kan masu Zanga- zanga, amma duk da haka sai da aka samu rasa rayuka sosai. Tuni dai gwamnati ta sanar da sabon tsarin biyan albashi ga ma’aikatan gwamnati a matsayin matakin farko na amsa bukatun masu Zanga- zangar.

 

3848889

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Iraki ، makoki ، kwanaki uku
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: