IQNA

23:26 - October 14, 2019
Lambar Labari: 3484154
Bangaren kasa da kasa, an shirya wani taro kan jawo hankulan musulmi zuwa yawon bude a Afrika ta kudu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a birnin Cape Town na Afrika ta kudu, an shirya wani taro kan jawo hankulan musulmi zuwa yawon bude a kasar, da aka yi ma take makon Halal A Afrika 2019.

James Vows daya ne daga cikin wadanda suka gabatar da jawabia  wurin taron, ya babyana cewa; birnin Cape Town yana tsohon tarihin zuwa musulmi a  cikinsa shekaru masu yawa da suka gabata,a  akn musulmi za su iya gudanar da ayyuka a bangarori daban-daban na karfafa yawon bude na musulmi.

Daga cikin muhimman abubuwan da mahukuntan kasar Afrika ta kudu suka baiwa muhimamnci domin jawo hankulan musulmi zuwa kasar a halin yanzu dai shi ne samar da abincin halal, wanda shi ne abu na farko da musulmi suke fara nema a duk inda suke tafi.

Baya ga haka kuma akwai tsare-tsare na wuraren tarihin kasar masu jan  hakula wadanda masu yawon bude kan ziyarta, wadanda za su zama daga cikin wuraren da za a rika kai musulmi domin bude ido a kasar.

 

3849837

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: