IQNA

23:54 - October 16, 2019
Lambar Labari: 3484158
Yara ‘yan kasa da shekaru 10 su 220 ne suka gudanar da gasar hardar kur’ani a birnin Darul Baida Libya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin libyaschannel.com cewa, a jiya aka kammala gasar hardar kur’ani a birnin Darul Baida wadda yara ‘yan kasa da shekaru 10 suka gudanar.

Bayanin ya ce yara mahardata yan kasa ad shekaru 220 maza da mata ne suka gudanar da gasar tsawon kwanaki goma, kuma sun fito ne daga cibiyoyin 60 na koyar da ur’ani a sassa na kasar.

Maikatar kula da harkokin addini ta kasar ce reshen Darul Baida ta dauki nauyin shirya gasar, wadda za a sanar da saamakonta ‘yan kwanaki masu zuwa.

 

3850396

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Libya ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: