IQNA

22:58 - October 29, 2019
Lambar Labari: 3484203
Firaminsitan kasar labanon, Saad Hariri, ya sanar da cewa zai mika takardar yin murabus din gwamnatinsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga Reuters yana bayar da rahoton cewa, wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da aka shiga kusan mako na biyu ana boren kin jinin gwamnatin kasar.

Mista Hariri ya sanar a yau Talata cikin wani jawabi a gidan talabijin cewa zai tafi fadar shugaban kasar domin mika masa da takardar murabus din gwamnatinsa, tare da kira ga ‘yan kasar dasu tattalin zaman lafiya.

Masu zanga zangar a kasar ta Labanon na masu zargin jami’an gwamnatin kasar da cin hanci da rashawa da kuma babakere da dunkiyar al’umma, wanda hakan yasa suka masa lamba kan dole ne sai gwanatin ta sauka, kamar yadda Hariri ya ce ya yi hakan ne domin karbakiran masu zanga-zanga.

 

3853259

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: