IQNA

23:00 - October 29, 2019
Lambar Labari: 3484204
Babbar jami’ar majalsar dinkin duniya a bangaren bincike ta bayyana cewa dole ne a hukunta ‘yan  Daesh a kasashensu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, babbar jami’ar majalsar dinkin duniya a bangaren ayyuan bincike na musamman a duniya Agnes Callamard, ta bayyana cewa dole ne a hukunta ‘yan ta’addan Daesh ‘yan kasashen waje da suke tsare a wasu gidajen kurkuku a Syria a cikin kasashensu na haihuwa.

Ta ce a halin yanzu akwai ‘yan Daesh masu tarin yawa ‘yan kasashen ketare da suke tsarea  wasu gidajen kurkuku a wasu yankuna da basa karkashin gwamnati, amma kawancen Amurka na yaki da ta’adanci na da iko da wasu kadan daga cikin yankunan.

Ta ce dole ne wadabda ake tsare da a wadannan wurare a mayar da su kasashensu domin hukunta.

Haka nan kuma ta yi ishara da kalubalan da ke attatre hakan, inda ta ce da dama daga cikinsu kasashensu sun kwace izinin zama ‘yan kasa daga gare su, kuma su ba ‘yan Syria ba ne, baya ga haka kuma wasunsu sun haifi yara da yawa a Syria, wanda hakan yasa dole ne majalisar dinkin duniya ta yi dogon nazari kan lamarin.

 

 

3853238

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: