IQNA

23:51 - November 03, 2019
Lambar Labari: 3484217
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Ayatullahi Sayyeed Aliyul Khamina’I ya bukaci a haramta tattaunawa tsakanin Iran da Amurka.

Kamfanin dillancin iqna ya habarta cewa, Jagoran yana fadar haka ne a yau Lahadi a lokacinda yake jawabi ga daliban jami’o’I a gidansa a nan Tehran.

Ayatullah Khamina’I’ ya kara da cewa daukar wannan matakin yana daga cikin hanyoyin hanasu kutsawa a cikin al-amuran kasar.

A cikin jawabinsa jagoran ya bayyana cewa kiyayya tsakanin mutanen Iran da kuma Amurka ta soma ne tun shekara 1953 a lokacinda Amurka ta jagoranci juyin mulki wanda ya kifar da gwamnatin zabebben Firai ministan kasar na lokaci Dr Mohammad Musaddiq.

Jagoran ya kara da cewa, da Iraniyiwa sun amince su tattauna da Amurkawa dangane da shirinta na makamai masu linzami, da mai yuwa zasu bukaci, misali ba zamu kera makami mai linzami da zai kai nisan kilomita 150 ba. Amma a halin yanzu muna da makamai masu linzami wadanda suke iya kaiwa tazarar kilomita 2000, wadanda kuma basa kuskure bararsu sai yan kadan.

Daga karshen jagoran ya bayyana cewa yakamata mutanen Iran su dauki darasi daga yadda Amurka take mu’amala da kasashen Cuba da Korea ta Arewa.

 

3854207

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: