IQNA

19:05 - November 24, 2019
Lambar Labari: 3484269
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron cika shekaru hamsin da kafa kungiyar OIC.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Saudiyya cewa, ana shirin gudanar da taron cika shekaru hamsin da kafa kungiyar OIC a birnin Jiddah.

An kafa kungiyar ta hadin kan kasashen musulmi ne a shekara ta 1969 tare da halatar mambobi kasashe 57 a birnin Rabat na kasar Morocco.

A karon farko a 1970 an gudana da taron ministocin hakokin waje na kasashe mambobin kungiyar a birin Jiddah na Saudiyya.

Tun daga shekara ta 2016 Yusuf Usaimin ne babban sakataren kungiyar, wadda take ci gaba da gudanar da harkokinta da suka hada da zama na shekara-shekara na shugabannin kasashen musulmi.

 

3859186

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، gudanar ، ci gaba ، OIC
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: