IQNA

Musawi Ya Mayar Da Martani Kan Taron Manama

19:15 - November 24, 2019
Lambar Labari: 3484271
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya mayar da martani kan taron larabawa da ya gudana Mana Bahrain.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Abbas Musawi ya yi allawadai da takunkumin da gwamnatin kasar Amurka ta dorawa ministan sadarwa da kuma kimiya na kasar Mohammad Jawad Azari.

Musawi ya kara da cewa wanda ya biduddugin tarihin kasar Amurka zai fahimci cewa ita ce kan gaba a kokarin dakile abokan hamayyarta a duniya.

Ya ce ko waya san yadda gwamnatin kasar Amurka take takurawa kamfanonin sadarwa na kasar wadanda suka hada da tweeter, facebook da sauransu don toshe shafuffukan abokan adawar gwamnatin kasar.

Kakakin ma’aikatar harkokinn wajen ya kammala da cewa Amurka, wacce ta yi fice a irin wannan halin ba ta cancanci bude baki tana zargin wasu kasashen duniya da take hakkin fadin albarkacin baki ba.

A ranar jumma’a da ta gabata ce gwamnatin kasar Amurka ta kakabawa ministan sadarwa na kasar Iran Mohammad Jawad Azari takunkumi tare da zargin shi da bada umurni a rufe yanar gizo a duk fadin kasar wanda ya hana masu tada zaune tsaye a kasar aika sakonni zuwa kasashen waje.

3859247

 

 

captcha