IQNA

Jagora: Al'ummar Iran Sun Sake Fallasa Makircin Makiya

11:08 - November 28, 2019
Lambar Labari: 3484278
Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran ya ce al'ummar kasar sun sake dakile makircin makiya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, ya bayar da rahoton cewa, da yake jawabi a gaban kwamadojin dakarun sa kai na kasar, jagoran juyin musulunci na kasar Iran Ayatullah sayyid Ali khamna’i, ya jinjinawa alummar kasar game da gagarumar nasarar da suka samu wajen tunkude makircin makiya na tayar da fitina a kasar ta hanyar fakewa da Zanga-zangar nuna rashin jin dadi game da karin farashin man fetur da gamnati ta yi.

Ganawar tasa ta zo ne adaidai lokacin da ake bukin makon dakarun sa-kai na kasa da aka kafa su shekara daya bayan cin nasarar juyin muuslunci a kasar a shekara ta 1979 karkashin jagorancin marigayi Imam khomaini yardar Allah ta tabbata gare shi.

Daga karshe jagoran ya kara da cewa batun karin farashin mai wata dama ce da makiya suke fake da ita domin cimma mummunan nufinsu , don haka an sanar da karin suka fara aiwatar da ita.

Daga karshe ya jinjinawa alummar kasar game da basira da suka nuna wajen dakile makircin makiya na haifar da tashin tashina.

A cikin makon da ya gabata ne wasu daga cikin al'ummar Iran suka fito domin nuna korafi kan wasu matsaloli na rayuwa musamman kara farashin man fetur.

Sai dai wasu masu wata manufa sun shiga cikin lamarin inda suka yi ta kone-kone da barnata dukiyoyin gwamanti da na jama'a da ma kisan mutane da jami'an tsaro, lamarin da jama'a suka nuna rashin amicewa da hakan.

 

3859897

 

captcha