IQNA

18:51 - December 01, 2019
Lambar Labari: 3484285
Bangaren kasa da kasa, Adel Abdulmahdi firayi ministan Iraki ya yi murabus daga mukaminsa a yau.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Kakakin gwamnatin Iraki ya sanar da cewa; Fira Ministan ya mika wa Majalisar dokokin kasar takardar sauka daga aiki.

Kakakin gwamnatin ta Iraki wanda kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya zanta da shi  ya ce fira minista Adil Abdul Mahadi ya cika alkawalin da ya yi na cewa zai kaddamar da takardarsa ta murabus ga majalisar dokoki.

A ranar juma’ar da ta gabata ne dai babban malamin shi’a na kasar ta Iraki, Ayatullah Sayyid Ali Sistani ya kira yi majalisar dokokin kasar da ta dauki matakan da su ka dace domin kawo karshen matsalar da ta fada ciki.

Al’ummar Iraki dai suna yin Zanga-zanga ne domin yin matsin lamba ga gwmanatin kasar ta yi murabus, bayan da cin hanci da rashawa su ka yi katutu a kasar.

3860824

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: