IQNA

Mahmud Shuhat Anwar: Kur’ani Ne Abin Afaharina

22:18 - December 12, 2019
Lambar Labari: 3484311
Mahmud Shuhat Anwar fitaccen makarancin kur’ani a Masar ya bayyana cewa kur’ani ne abin alfaharin rayuwarsa.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a tattaunawarsa ta tashar Ahkbar Masar ya bayyana cewa, babuabin da yafi kur’ani a wurinsa doin shi ne komain a rayuwarsa.

Ya ci gaba da cewa, littafin Allah shi ne abin da yafi soyuwa ga al’ummar Masar, kamar yadda shi ma yake alfahari da hakan.

Mahmud Shuhat Anwar ya karbi shadar dokta ta bangirma daga jami’ar New York da ke kasar Amurka, sakamakon tasirin ira’arsa da kwarewarsa a wanann fage.

Mutane 3 ne suka musulunta  akasar Afrika ta kudu, yayin da wasu uku kuma daga Birtaniya da kuma wani daga Amurka suka musulunta bayan da suka saurai karatunsa na kur’ani.

A watan Ramadan da ya gabata ma wasu mutane 10 daga kasar Ukraine sun musulunta a lokacin da suka halarci wani majalisa da yake yin karatun kur’ani.

3863645

 

https://iqna.ir/fa/news/3863645

 

 

 

captcha