IQNA

21:57 - December 16, 2019
Lambar Labari: 3484323
Bangaren kasa da kasa, Shugaban Najeriya ya nada sabon Amirul Hajj na wannan shekara da muke ciki.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Hassan Zikrullah daga jihar Osun a matsayin sabon Amirul Hajj na wannan shekara domin aikin hajjin bana.

Sauran mambobin kwamitin sun fito daga jihohin Kano, Bauchi, Edo, Ogun, Niger, Borno, Sokoto da kuma Delta, inda aka mika sunayen nasu ga majalisar dattawa domin tantance su.

Najeriya dai it ace kasar da tafi yawan jama’a  anahyar Afrika, inda take da mutane da suka kai miliyan 200 a halin yanzu.

A kowace shekara masu zuwa aikin hajji daga Najeriya ne suka fi yawa daga kasashen Afrika, kamar yadda kuma take kashi 55 cikin dari na mutanen kasar musulmi ne.

Ana sa rana kammala ayyukan rijistr maniyyata na wanann shekara a cikin ‘yan watanni masu zuwa a tarayyar Najeriya.

 

https://iqna.ir/fa/news/3864308

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kamfanin dillancin labaran iqna ، iqna ، Najeriya ، Bauchi
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: