IQNA

An Saka Sadakin Hardar Kur’ani A Kasar Masar

10:21 - December 22, 2019
Lambar Labari: 3484335
Bangaren kasa da kasa, an saka sadakin wata yarinya ya zama hardar izihi biyar da salati dubu 100.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, an yada wani labari a yanar gizo kan sadakin hardar kur’ani da salati ga manzon Allah.

Bayanin ya ce wannan yarinya tana karatun jami’a ne, kuma an yi hakan ne domin kara karfafa gwiwar iyaye da su rage yawan tsawwala sadaki ga masu neman ‘yayansu da aure.

Mahaifin yarinyar ya bayyana cewa, babban abin da yake da muhimmanci a wurinsa shi ne samun miji na gari ga diyarsa, ba yawan kudin sadakin da za a bayar domin aurenta ba.

Islam Abdunnabi shi ne wanda yake neman auren wanann yarinya, ya bayyana cewa; za a daura musu aure da yardarm Allah idan ya kammala hardar juzu’i biyar, da kuma rubutun salatin manzon Allah.

 

https://iqna.ir/fa/news/3864880

captcha