IQNA

15:55 - January 11, 2020
Lambar Labari: 3484404
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da sallar janaza ta sarki Qabus na kasar Oman a yau.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, a yau ne aka gudanar da sallar janazar marigayi sarki Qabus na kasar Oman, wanda ya rasu jiya yana dan shekaru 79 a duniya bayan fama da rashin lafiya.

Sarki Qabus ya dare kan mulkin kasar Oman bayan mahaifinsa, inda aka sanya ranar 23 ga watan Yuli ta zama muhimmiyar rana a kasar, saboda  aranar ne ya karbi mulkin kasar.

Sarki Qabus ya taka rawa wajen ganin ya mayar da hankali ga ayyukan sulhunta rikice-rikice tsakanin kasashe, musamman na yankin gabas ta tsakiya.

Za  aiya kallon bidiyon janazar a nan: -

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3870652

Abubuwan Da Ya Shafa: kamfanin dillancin labaran iqna ، iqna ، sarki Qabus ، Oman ، janaza
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: