IQNA

21:22 - January 14, 2020
Lambar Labari: 3484415
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana Birtaniya a matsayin wata babbar ‘yar amshin shata ga Amurka.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, Muhammad Jawad zarif minsitan harkokin wajen na Iran ya yi kira ga kasashen turai da su cika alkawalin da ke wuyansu dangane da yarjejeniyar Nukiliya maimakon zama masu yin biyayya ga Amurka.

Da safiyar yau Talata ne dai ministan harkokin wajen na Iran ya wallafa a shafinsa na twitter cewa;

1) Shin ba abin kunya ne ba? Birtaniya tana maimaita abinda Amurkan take fada ne kamar tsuntsun Aku, shin wannan ba kuma ba tarayya da ita ce a cikin dukkanin ayyyukan ta’addanci da take yi a cikin wannan yankin ba tare da tunani ba?

2) Abin kunya na karshe wanda Birtaniya ta yi, shi ne biye wa Amurka da yi ma ta rakiya a yakar kasar Iraki. Sai dai abin tambaya anan shi ne me hakan ya jawo ma ta.

 

https://iqna.ir/fa/news/3871442

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Amurka ، Zarif ، caccaki ، Birtaniya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: