IQNA

21:30 - January 14, 2020
Lambar Labari: 3484416
Bangaren kasa da kasa, an ji karar harbe-harbea  cikin wasu barikokin soji da ke bababn birnin kasar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, rahotanni daga Sudan na cewa an jiyo karan harbe harbe masu tsanani a wasu barikin jami’an tsaro biyu a Kartoum babban birnin kasar, inda daga bisani aka toshe hanyoyin dake kai wa ga wuraren da aka jiyo harbe harben.

Babu dai karin bayyani nan take kan ainahin abunda ya faru a cewar kamfanin dilancin labaren faransa amma ganau sun shaida cewa lamarin ya faru ne a wata barikin jami’an tsaro da ke unguwar Riyadh a arewacin babban birnin kasar, sai kuma a barikin jami’an tsaro ta Bahari.

Barikin jami’an tsaron guda biyu, na dauke da tsahuwar hukumar leken asiri ta kasar ta lokacin mulkin hambararen shugaban kasar Omar el-Bechir, wacce yanzu ta koma babbar hukumar leken asiri ta kasar.

An bayyana cewa hukumar ta taka mahimmiyar rawa wajen murkushe masu boren da ya kai ga hambarar da mulkin shugaba El-Bashir a watan Afrilu na shekarar data gabata.

 

https://iqna.ir/fa/news/3871672

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: