IQNA

21:57 - January 16, 2020
Lambar Labari: 3484419
Bangaren kasa da kasa, an yi wa babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sistani aikin tiyata.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, kamfanin dillancin labaran saum,aria News ya habarta cewa, a yau an yi wa babban malamin addini na kasar Iraki Ayatollah Sistani aikin tiyata cikin nasara.

Rahoton ya ce bayan kamala aikin tiyatar an fitar da malamin daga dakin tiyata zuwa inda za a kula da shi.

Tun bayan sanar da faruwar lamarin, babban ofishin malamin ya bayyana cewa a jiya ne da dare karfarsa ta hagu ta samu matsalar karaya, kuma tuni aka bukaci addu’a daga al’umma kan samun lafiyarsa.

Bayanin ya kara da cewa, ya zuwa yanzu miliyoyin jama’a ne suka yada labarin kafofin sadarwa na zumunta, tare da taya shi addu’a kan Allah ya ba shi lafiya, kamar yadda tuni gwamnatin Iraki ta sanar da cewa an dauki matakai na bin kadun lamarin ta bangarorin da suka dace.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3872073

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Sistani ، babban malami ، Iraki
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: