IQNA

Almanar: Shin An Raba Danyen Man Libya A Taron Berlin?

23:57 - January 21, 2020
Lambar Labari: 3484438
Bangaren kasa da kasa, an kammala zaman taron da aka shirya a birnin Berlin na Jamus da sunan warware rikicin kasar Libya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA, shafin Almanar ya bayar da bayanin cewa, shugabannin manyan kasashen duniya da suka halarci taro kan rikicin Libya a birnin Berlin na Jamus sun yi kira da a kawo karshen tsoma baki a cikin rikicin Libya da kasashen waje ke yi, suna masu alkawarin kafa kwamitin da zai bibiyi sakamakon taron bayan kammala shi.

Haka nan kuma shugabannin manyan kasashe masu fada a ji da sauran kasashen da batun ya shafa, sun hadu ne a Berlin, da sunan lalubo hanyar warware rikicin Libya cikin ruwan sanyi ba tare da ci gaba da tashin hankali ba.

Bayan nan kuma wakilai daga majalisar dinkin duniya da Tarayyar Turai da Tarayyar Afrika da Kungiyar kawancen kasashen Larabawa, da shagabannin bangarorin dake rikici da juna Libiyar, da suka hada da Khalifa Haftar, dake da karfin iko a yankin gabashin kasar da Fayez al-Sarraj, shugaban gwamnatin hadin kan kasa dake samun goyan majalisar dinkin duniya su ma sun halarci taron na birnin Berlin.

Daga karshe kumasanarwar bayan taron da aka fitar, ta ruwaito shugabannin na cewa, suna jadadda kudurinsu, na martaba cikakken iko da 'yanci da yankuna da hadin kan kasar Libya, Inda suka ce tsarin siyasa irin na kasar Libya, karkashin jagorancin kasar ne kadai zai iya kawo karshen rikicin wanda Libya take fama da shi.

Haka nan kuma shugabannin sun ce suna kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, su kauracewa duk wani abu da ka iya ta'azzara rikicin ko kuma sabawa takunkumin kwamitin sulhu ko shirin tsagaita bude wuta, ciki har da samar da kudade ga ayyukan soji ko horar da sojojin haya wadanda suke yaki a cikin kasar.

Duk wannan na daga cikin abin da aka bayyana a zahiri, amma abin da yake jawo alamar tambaya shi ne, kasashen ad suka haddasa rikicin kasar ta Libya kuma su ne suke jagorantar zaman, wanda hakan ke sa shakku kan cewa wata kila an dai shirya taron sulhuntawa ne a zahiri, amma bayan fage ana watandar rijiyoyin man kasar Libya ne.

 

https://iqna.ir/fa/news/3873079

captcha