IQNA

23:47 - February 05, 2020
Lambar Labari: 3484488
Gwamnatin kasar hadaddiyar daular larabawa ce ta shirya ganawa tsakanin shugaban riko na Suda da kuma Netanyahu.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin Aljazerra ya bayar da rahoton cewa, ganawar da aka yi a tsakanin Natenyahu da shugaban majalisar koli ta mulkin kasar Sudan Abdulfattah al-Burhan, a kasar Uganda tsararren lamari ne, wanda gwamnatin hadaddiyar daular larabawa ce ta shirya ganawar.

Rahotanni da kafofin yada labaran Isra’ila suka bayar sun tabbatar da cewa; tun kafin wannan lokacin an yi wata ganawar share fage a tsakanin mai bayar da shawara akan harkokin tsaro ga Netanyahu Ma’ir Bin Shabat, da wasu manyan jami’an kasar Sudan, inda su ka cimma matsaya akan cewa Netanyahu zai shiga gaba domin Amurka ta dauke wa Sudan takunkumai.

Majiyar ta ce a halin yanzu kasar Sudan ta shiga cikin sahun kasashe masu sassauci irin su Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da su ke da kusanci da gwamnatin yahudawan Isra’ila.

Dan rahoton tashar talabijin tasha ta sha daya ta Isra’ila Amihaya Shataynil ya bayyana cewa; Aiki na farko da za a fara yi shi ne mayar da ‘yan gudun hijirar Sudan zuwa gida. Haka nan kuma Sudan za ta rika bayar da dama ga jiragen sama na Isra’ila su rika bi ta sararin samaniyarta zuwa wasu kasashe.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3876400

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: