A cikin wani rahoto da tashar CNN ta bayar ta bayyana cewa, sakamakon yadda aka fara samun yaduwar cutar nan ta corona a wasu yankunan yankin gabas ta tsakiya, mahukuntan Saudiyya sun dakatar da bayr da izinin shiga kasar domin aikin Umrah.
Ma’aikatar kula da kiwon lafiya ta kasar tare da hadin gwiwa da ma’aikatar kula da harkokin ayyukan haji da Umra ne suka cimma matsaya guda kan wannan batu, domin kaucewa kamuwa da cutar a yayin taron umar wanda yake hada mutane da dama a wuri guda.
Wasu bayanai sun ce an samu yaduwar cutar nea cikin birnin Makka, wanda hakan yasa mutane suka yi ta mika kira ga mahukuntan kasar ta Saudiyya da a dauki matakin dakatar da ayyukan na umrah.
Duk kuwa da cewa a hukumance babu wani bayani tabbatacce kan yaduwar cutar corona a Saudiyya, amma wasu daga cikin makwabtanta kamar, Kuwait, Bahrain, da UAE, duk an samu bullar cutar.