IQNA

An Rufe Ajujuwan Kur’ani A Kasashen Oman Da Morocco

15:01 - March 15, 2020
Lambar Labari: 3484624
Tehran (IQNA) an rufe ajujuwan koyar cda karatun kur’ani a kasashen Oman da Morocco sakamakon yaduwar corona.

Shafin yada labarai na shuoon.om ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini ta Oman ta sanar a yau cewa, an rufe dukkanin ajujuwan koyar da karatun kur’ani da suke karkshin makarantu na wannan ma’aikata, amma za a ci gaba da karatun ta hanyar yanar gizo.

Wanann mataki ya zo ne biyo bayan sanar ad rufe dukaknin cibiyoyin addini da tarukan addini da ake gudanarwa.

Haka nan a kasar Morocco ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar ta sanar ad rufe makarantu baki daya da suka hada na firamare ko sakandar da na gaba da sakandare da jami’oi da sauran cibiyoyin ilimi a fadin kasar har zuwa wani lokaci a nan gaba.

Sanarwar ta ce a wasu bangarorin za a iya yin karatun ta hanyar yanar gizo.

 

3885423

 

Abubuwan Da Ya Shafa: morocco oman makarantu addini
captcha