IQNA

23:04 - March 24, 2020
Lambar Labari: 3484651
Tehran (IQNA) mutane da dama ne suka yi ta yin kabbarori a daren jiya a birnin Qods domin a matsayin neman Allah ya kawar musu da corona.

Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, a karshen daren jiya Litinin 23 ga watan Maris, mutane da dama sun hau kan rufin gidajens a birnin Qods suna kabbarori, suna masu rokon Allah ya kawar da bala'in corona ga dukkanin al'ummar musulmi.

Domin kauce wa yaduwar cutar corona, a jiya an rufe masallacin aqsa baki daya, tare da dakatar da dukkanin ayyukan ibada  acikinsa.

3887143

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: