IQNA

Hamas Ta Ce Isra’ila Ba Ta Da Makoma A Falastinu

23:30 - April 09, 2020
Lambar Labari: 3484694
Tehran (IQNA) kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas ta ce Isra’ila ba ta da makoma a cikin Falastinu.

Kamfanin dillancin labaran safa na Falastinu ya bayar da rahoton cewa, Hazim Qasem kakakin kungiyar Hamas ya fadi yau cewa, bisa la’akari da ayyukan yaki da kisan kiyashin da yahudawan Isra’ila suka kan dubban daruruwan Falastinawa, wannan yasa Isra’ila ba ta da makoma a cikin Falstinu.

Kakin na Hamas ya yi wanan furuci a lokacin tunawa da zagayowar kisan kiyashin Deir Yasin.

Shekaru saba’in da biyu  da suka gabata a rana irin ta yau wasu kungiyoyin yahudawan Sahyoniya karkashin wasu fitattun yahudawan Isra’ila sun afkawa garin Dair-Yasin a kasar Falasdinu inda suka yiwa Palasdinawa a garin kisan kiyashi.

Kungiyoyin ‘yan ta’adda na yahudawan Isra’ila kimani sun kashe daruruwan Faladinawa a garin na Dair-Yasin, wanda yake da mazauna kimanin dubu hudu.

Manufar wannan kisan kiyashin dai ita ce korar Falasdinawa ko kuma halaka su don samun damar shelanta kafuwar Isra’ila a cikin watan Mayu na waccan shekarar.

 

3890467

 

 

captcha