Shafin yada labarai na jaridar Yaum sabi a kasar Masar ya bayar da rahoton cewa, a jiya sheikh Anawar Shuhat Anwar ya gudanar da karatu kur’ani. Shi da ne marigayi sheikh Shuhat Muhammad Anwar, an haife shi a ranar 29 ga watan Mayun 1978 a kauyen Kafar Wazir a cikin gundumar Diqahiya.
Tun yana karami ya hardace kur’ani mai tsarki tare da taimakon mahaifinsa da kuma tarbiyarsa.
Ya kasance yana gabatar da karatun kur’ani a cikin gidan radiyon Masar tsakanin shekaru 2004 har zuwa shekara ta 2008.