IQNA

Bayanin Azhar Dangane Da Ranar Yara Ta Duniya

23:55 - June 13, 2020
Lambar Labari: 3484892
Tehran (IQNA) babbar cibiyar musulnci ta kasar Masar ta Azhar ta fitar da bayani kan ranar yara ta duniya.

Shafin yada labarai na Bawwaba News ya bayar da rahoton cewa, a yau babbar cibiyar musulnci ta kasar Masar ta Azhar ta fitar da bayani kan ranar yara ta duniya tare da bayyana ranar da cewa tana da matukar muhimmanci.

Bayanin ya ci gaba da cewa, ranar yara ta duniya wadda ta yi daidai da 12 ga kowane wata na yuni, tana a matsayin wata rana mai muhimmanci ga dkkanin al'ummomin duniya.

Azhar ta ce yara su ne tubalin ginin kowace al'umma saboda haka matsayin a cikin kowace al'umma yana da matukar muhimmanci.

Daga karshe bayanin ya kirayi al'ummomi musamman musulmi da su dauki lamarin yara da tarbiyars da matukar muhimmanci a cikin lamrra na zamantakewa, saboda irin gudunmawar da za su bayar a rayuwarsu ta gaba.

 

 

3904501

 

captcha