IQNA

Wani Mutum Ya Rubuta Kur’ani Da Kyakkyawan Rubutu A Libya

22:33 - June 14, 2020
Lambar Labari: 3484893
Tehran (IQNA) Sheikh Ahmad Muhammad Al-ghali Khairat bin Aukal ya rubuta kur’ani mai tsarki a cikin shekaru 4 a Libya.

Shafin yada labarai na afrigatenews ya bayar da rahoton cewa,  Sheikh Ahmad Muhammad bin Aukal daga yankin Alfujaij mujahidah kasar Libya, ya rubuta kur’ani mai tsarki a cikin shekaru hudu.

Ya rubuta kur’anin bisa ruwayar Qalun bin naïf, kamar yadda kuma ya tsara rubutuna  cikin salo mai kayatarwa.

Kwafin kur’ani yana shafuka 621, kamar yadda ya dauki watanni 7 yana kayata shafukansa, haka nan kuam yak an yi alwala duk lokacin da zai yi rubutun.

 

3904614

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: watanni Sheikh Ahmad Muhammad kasar Libya
captcha