IQNA

Ilhan Umar ta Sanar Da Mutuwar Mahaifinta

23:06 - June 16, 2020
2
Lambar Labari: 3484901
Tehran (IQNA) ‘yar majalisar dokokin Amurka Ilhan Umar ta sanar da rasuwar mahaifinta a yau.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, Ilhan Umar yar majalisar dokokin Amurka ta sanar da rasuwar mahaifinta a shafinta na twitter kamar haka:

Ga Allah mu ke kuma lallai mu gare shi za mu koma

Ina bakin cikin sanar da rasuwar mahaifina wanda ya rasu a daren jiya Litinin bayan da ya kamu da cutar corona.

Ihan Umar sun zo Amurka ne tare da mahaifinta a cikin shekara ta 1995, bayan da suka yi gudun hijira daga kasar Somalia zuwa Amurka, inda suka zauna a garin Minneapolis.

Ihan Umar da Rashida Tlaib musulmi ne da suka tsaya takarar majalisar wakilan Amurka a shekara ta 2018, kuam suka samu nasara.

3905249

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: ilham umar ، Somalia ، gudun hijira ، Amurka ، minnesota ، minneaplis ، wakilan
Wanda Aka Watsa: 2
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
0
Allah ya sada shi da Muhammadur Rasulullah S.A.W
Ba A San Shi Ba
0
0
Allah ya sada shi da Muhammadur Rasulullah S.A.W
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha