Shafin yada labarai spotrsnewsps ya bayar da rahoton cewa, wani masallaci a yankin Dammam na Saudiyya ya samar da hanyar karatun kur'ani ta Digital cikin sauki ga masu bukata.
Bayanin ya ce mutane za su iya shiga cikin tsarin ne ta hanyar samun lamba wadda za a ba su, da kuma hotunasu, ta yadda za su iya shiga kai tsaye.
Tsarin dai ya kunshi karatun kur'ani daga makaranta daban-daban, da kuma tarjama zuwa harsuna daban-daban na duniya, ta yadda mutum zai iya amfana da su.